Yan bindiga sun kashe dan sanda da dan bijilanti a Sokoto

0
58

Wasu yan bindiga sun hallaka jami’in dan sanda da dan Bijilanti yayin da suke ran gadi a jihar Sokoto.

Lamarin ya faru da misalin karfe 3 na daren lahadi, akan hanyar Kwanan Milgoma, daura da hanyar zuwa Bodinga.

Duk da cewa mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar bai bayyana komai akan faruwar hakan ba, amma wani babban jami’in dan sandan daya nemi a sakaya sunan sa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ku Karanta: Gwamnatin Sokoto ta tube Uwayen Kasa 15 daga kujerunsu

Yace jami’an sun yi taho mu gama da yan bindigar wanda suke tafe a cikin wata mota kirar Hilux.

A cewar sa, yan bindigar sun hadu da jami’an tsaron masu bincikar ababen hawa akan titi inda nan take suka bude musu wuta, tare da yin awon gaba da binding kirar AK-47 da harsasai.

Bayan kashe jami’an tsaron an kai gawar su, zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo, dake jihar Sokoto.

Jihar Sokoto dai na daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro musamman yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Idan za’a iya tunawa ko a yan makonnin da suka gabata sai dai yan garkuwa da mutane suka hallaka sarkin Gobir, bayan yin garkuwa dashi.

Yan Boko Haram sun bankawa Shaguna da gidaje wuta a jihar Yobe

Wasu da ake kyautata zaton mayakan boko haram ne sun kwashe kayayyakin Shaguna tare da banka musu wuta a kauyen Mafa dake karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe.

Jami’in yada labaran rundunar yan sandan jihar DSP Dungus Abdulkarim, ne ya sanar da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN hakan a yau litinin.

Zuwa yanzu ba’a san adadin mutanen da yan boko haram din suka hallaka ba, a harin na karfe 4 na daren lahadi, a cewar sa.

Wasu mazauna kauyen Mafa Babagana Goni da Bako Ibrahim ne suka kai rahoton harin ga babban ofishin yan sandan yankin.

Mutanen kauyen sun ce mayakan sun zo akan babura fiye da 50, dauke da muggan makamai, Kuma nan take suka kone gidaje da shagunan mutane.

Bayan kisan da suka yi, rundunar yan sandan tace mayakan sun watsa wasu takardu dauke da rubutun larabci.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa ko a ranar juma’ar data gabata sai dai mayakan suka kai hari wata makaranta mai zaman kanta a Geidam, inda suka kashe dalibai biyu da jikkata guda daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here