Yan bindiga sun hallaka mutum 30 a Zamafara

0
132

‘Yan bindiga a jihar Zamfara sun ƙaddamar da munanan hare-hare a jihar Zamfara, lamarin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 30 ciki har da wani fitaccen malamin addini.

An kai hare-haren a ranar Alhamis a ƙauyukan Gidangoga a yankin ƙaramar hukumar Maradun da Bilbis a yankin ƙaramar hukumar Tsafe.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa da farko ‘yan bindigar sun fara kai hari garin ƙauyen Gidangog ne kan wasu manoma da ke aikin share gonakinsu, a shirye-shiryen da suke yi na tunkarar daminar bana.

”A harin ne kuma ‘yan bindigar suka kashe Mallam Makwashi Maradun Mai Jan Baki, fitaccen malamin addinin Musulunci a gonarsa”, in ji jaridar.

Mallam Makwashi, shi ne mai jan baƙi a tafsirin da ake gabatarwa a masallacin Juma’a na Maradun.

Haka kuma da maraice ‘yan bindigar suka ƙaddamar da wani mummunan harin a garin Bilbis na yanƙin ƙaramar hukumar Tsafe, tare da kisan aƙalla mutum 20.

Hare-haren sun jefa al’ummar yankin cikin zulumi da fargaba.

Jihar Zamafar da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da matsalolin ‘yan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here