Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe mako guda babu labarinsa

0
172

Bayan shafe mako guda ba tare da jin duriyar sa ba, shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya dawo gida.

Rashin sanin takaimaiman hali ko kuma inda shugaban yake na tsahon mako guda ya fara haddasa cecekuce musamman game da yanayin lafiyar sa, yayin da aka fara nuna yatsa ga masu Magana da yawunsa tare da jifan su da tambayoyi kan inda shugaban yake.

Ganin karshe da aka yiwa Tinubu cikin bainar jama’a shine wajen taron tattalin arziki na birnin Riyadh din Saudi Arabiya, taron da ya halarta daga kasar Netherlands.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here