Yarjejeniyar da muka amince ce dama ta karshe ga Isra’ila – Hamas

0
160

Wani babban jami’i a ƙungiyar Hamas ya ce zuwan da wakilansu za su yi birnin Alƙahira domin tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta ita ce dama ta ƙarshe ga Isra’ila wajen sakin mutanenta da Hamas din ta yi garkuwa da su.

Da yake magana ga kamfanin dillancin labari na AFP, jami’in ya ce masu sasantawa na Hamas da farko sun soke tafiya zuwa Alƙahira daga Qatar.

Jami’in na Hamas ya ce nan gaba kaɗan za su tafi zuwa Alƙahira.

Harwayau, jami’in na Hamas ya ce ƙudirin firaiministan isra’ila, Benjamin Netanyahu na shiga Rafah ya nuna cewa Netanyahu da sojojin Isra’ila suna son waɗanda ake garkuwar da su su mutu.

“Wannan ita ce damar Netanyahu da iyalan Yahydawa fursunoni ta ƙarshe domin mayar da yaransu gida.” In ji jami’in.

Hamas ta yi garkuwa da mutum 252 lokacin harin da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba, sannan kuma ba a san inda mutum 128 suke ba. Isra’ila ta ce tana kai hare-hare ne “a Rafah da manufar neman mutanen da aka yi garkuwa da su a maɓoyar ‘yan ta’adda.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here