Karin dakarun sojin Rasha sun isa Nijar

0
185

Wasu ƙarin jami’an soji masu horaswa na kasar Rasha sun isa Nijar a ranar 4 ga watan Mayu, makonni bayan ƙasar ta karɓi dakaru 100 na rundunar sojin Afirka da na tsaro ta jiragen sama, kamar yadda shafin jaridar ActuNiger ya ruwaito. 

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da dangantaka ke kara ƙulluwa tsakanin shugabannin sojojin Nijar da fadar Kremlin ta Rasha. 

A cewar ActuNiger, jirgin sama na sojan Rasha na uku ya sauka a Yamai babban birnin kasar ɗauke da wani gungun jami’an soji masu horaswa, da kayan aiki, da kuma kayan agaji.

“Sojoji masu horaswa” da Moscow ta aiko ƙarkashin yarjejeniyar hadin-gwiwa ta tsaro za su taimaka wajen horar da jami’an tsaron Nijar don fuskantar “rikitattun kalubale” da dabarun yaki.

Nijar ta soke yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka, sannan ta kuma kori dakarun Faransa daga kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here