Ukraine za ta iya amfani da makaman Burtaniya a cikin Rasha – Cameron

0
167

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, David Cameron ya ce ƙasar Ukraine na da zaɓi ta fahimci yadda za su yi amfani da kayan yaƙin Burtaniya su kuma kai hari kan Rasha.

Mista Cameron ya faɗi hakan ne yayin wata ziyara a birnin Kyiv, ya ƙara da cewa Burtaniya za ta samar da fam biliyan uku a duk shekara.

“Kamar yadda Rasha ke kai hare-hare cikin Ukraine, za ka fahimci dalilin da ya sa Ukraine ke son kare kanta,” in ji Lord Cameron.

Ƙasar Rasha ta yi allawadai da abun da ta kira “ƙarin wani kalami mai haɗari”.

Mista Cameron kai tsaye bai goyi bayan tunanin Ukraine ta yi amfani da kayan yaƙin Burtaniyar domin yaƙar Rasha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here