Kotu ta ci tarar Trump dala 9,000 kan saba umarninta

0
152
Donald Trump
Donald Trump

Alkalin da ke sauraron shari’ar Donald Trump kan zargin biyan tauraruwar fina-finan batsa kuɗi domin ta ɓoye mu’amalr da suka yi a birnin New York na Amurka, ya samu tsohon shugaban na Amurka da laifin ci gaba da saɓa wa dokar kotu. 

Umarnin ya haramta wa Trump yin magana a bainar jama’a da yaɗa wa a shafukan sada zumunta game da mutanen da ke da hannu a shari’ar.

A ranar Talata, alkalin kotun Juan Merchan ya ce Trump ya saɓa wa umarnin sau tara. 

Kotun ta ci tarar Trump dala 1,000 kan kowanne saɓa umarni.

Masu gabatar da ƙara sun ba da cikakken bayani game da yiwuwar saɓa wa kotun har sau 14, kuma Merchan na iya yanke shawara a zaman da za a yi ranar Alhamis.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here