Gwamnatin Edo  ta sanar da mafi karancin albashin N70,000 ga ma’aikatan jihar

0
166

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikatan gwamnati daga N30,000 zuwa N70,000 a jihar.

Gwamna Obaseki ya bayyana haka ranar Litinin lokacin da yake ƙaddamar da ginin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar. 

A cewar gwamnan, sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu.

Matakin gwamnan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙwadagon ke matsa wa gwamnatin tarayya lamba don ta ƙara mafi ƙarancin albashin domin rage wa ma’aikata raɗaɗin hauhawar farashi.

NLC da TUC sun nemi gwamnati ta mayar da mafi ƙanƙantar albashin ya zama N615,000.

Tun a watan Janairu ne gwamnatin Bola Tinubu ta kafa kwamitin mutum 37 da ke da wakilci daga ɓangarori da dama – gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyar ƙwadago.

Kwamitin zai tattauna domin tsayar da mafi ƙarancin albashin da zai gabatar wa gwamnati domin amincewarta.

A lokacin ƙaddamar da kwamitin, mataimakin shugaban ƙasa, Kassim Shettima ya nemi kwamitin ya gaggauta wajen cimma matsaya, ya kuma miƙa rahotonsa da wuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here