Ƙyanda ta ‘kashe yara 19’ a Adamawa

0
188

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Mubi ta Arewa sun ce aƙalla yara 19 ne suka mutu sakamakon bullar wata rashin lafiya da ake zargin kyanda ce.

Kyanda dai wata cuta ce da take yaɗuwa ta yi illa kuma musamman tsakanin yara ƙanana.

Daga cikin illar da take haifarwa akwai makanta da kumburin kwakwalwa da gudawa da nunfashi da kyar.

Da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, kwamishinan lafiya na jihar Felix Tangwami ya ce sama da yara 200 yanzu haka sun kamu da cutar a ƙaramar hukumar.

Ya ce a ranar Asabar ma an samu bullar cutar a Yola babban birnin jihar, abin da ya janyo aike wa da magunguna da kuma ma’aikatan lafiya ga kauyukan da abin da ya shafa.

Ya yi alƙawarin za a yi  a garzaya da yaran da suka kamu zuwa asibitoci.

Kwamishinan ya ce za a aika da jami’an lafiya ƙaramar hukumar Mubi da Gombi inda aka ƙara samun bullar cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here