Yan bindiga sun kashe mutum 3, tare da garkuwa da 8 a Kaduna

0
155
Kaduna

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu takwas a wani hari da suka kai kauyen Hayan Habuja a Kakangi da ke karamar hukumar Birnin-Gwari na jihar Kaduna

Sabon harin na zuwa ne kwanaki biyar bayan da ‘yan bindiga suka kashe wasu mutum 23 a anguwan Danko kusa da Dogon Dawa na karamar hukumar. 

Sakataren wata kungiya ta Birnin-Gwari BEPU, Abdulrrashid Abarshi ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa garin ne da misalin karfe 3 na ranar Talata. 

Ya ce an harbe mutum biyu nan take yayin da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da wasu mutum huɗu. 

“Lokacin da ‘yan bindigar suka zo fita kauyen Hayan Abuja, sun kashe wani mutum wanda ya fita neman itace da kuma yin garkuwa da mutane hudu,” in ji Abarshi.

Ƙungiyar ta BEPU ta yi kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen daukar matakai na shawo kan matsalar tsaro a yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here