Kiyayyar da ake yi wa ’yan sanda na shafar harkar tsaro a Najeriya

0
182
Yan sanda
Yan sanda

Shugaban kwamitin da ke taimaka wa ayyukan ‘yan sanda na kasa (PCRC), Mogaji Olaniyan, ya yi kira da a gaggauta magance abin da ya kira ƙiyayya ga jami’an ‘yan sandan Najeriya.

Olaniyan ya bayyana lamarin a matsayin mai ban tsoro, yana mai nuna cewa ƙiyayyar da ake yi wa jami’an ’yan sanda ta kasance cikin abubuwan da ke shafar tsaron ƙasar nan.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin bikin cikar zaman kwamitin karo na 40 da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin Jihar Oyo.

Olaniyan, wanda ya yi Allah wadai da wannan ƙiyayyar da ake yi wa ’yan sandan, ya ce PCRC na ƙulla alaƙa ta dindindin a tsakanin al’umma da ‘yan sanda domin kawo ƙarshen wannan mummunan tunani.

Ya kuma jaddada cewa dole ne a magance wannan ɓacin rai don samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin jama’a da ‘yan sanda, tare da samar da tsaro a faɗin ƙasar nan.

Olaniyan ya ce, “Muna kira ga mutane su nuna soyayyarsu ga ‘yan sandan Najeriya, abin da jama’a suka rasa ke nan. Tun muna yara mun haifar da gaba tsakanin yaran mu da ‘yan sandan Najeriya.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here