Madrid ta haye zagayen ɗaf ta karshe na gasar UCL bayan doke City

0
274

Real Madrid da Bayern Munich sun bi sahun Paris Saint Germain da Brusia Dortmund zuwa wasan daf da ƙarshe na gasar zakarun turai.

Real Madrid ta dauki fansa kan Manchester City da ci 4-3 a bugun fanariti, bayan da ta shi wasa 1-1 a Etihad daren Laraba.

Rodrygo ne ya fara ci wa Madrid ƙwallo a mintuna 12 da soma wasa kafin Kevin De Bruyne farke wa City a mintuna 76 aka ƙarkare kunnen doki 1-1, wato 4-4 jimilla gida da waje, abin da ya sa aka je ƙarin lokaci, har aka kai bugun finareti.

Sai dai mai tsaron ragar Real Madrid Andriy ya kawo ƙarshen bajintar da masu rike da kambin City suka nuna amatsayin mafi tsaron baya na gasar bayan tare ƙwallayen Bernardo Silva da Mateo Kovacic a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here