Sojoji sun kama ‘mai sayar wa yan bindiga makamai’ a Taraba

0
171
Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe wani ɗan bindiga tare da kama wani mutum da ake zargi da sayar da makamai ba bisa ƙa’ida ba a wani samame da dakarunta suka kai jihohin Benue da Taraba.

A samamen, sojojin sun daƙile yunƙurin sace mutane kamar yadda daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana a sanarwar da ya fitar. 

A jihar Taraba, sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan sintiri sun kama mutumin da ake zargi da sayar wa ƴan bindiga makamai ba a tashar mota ta Jalingo.

Kamen nasa kuma ya sa an kama wasu mutanen da suke gudanar da ayyukan tare, in ji sanarwar.

Rundunar ta kuma gano wasu bindigogi ciki har da ƙirar gida, da mota ƙirar Peugeot, da wayoyin hannu biyar, sai kunshin alburusai, da kuma babur, a cewarta. 

A wani samamen na daban, sojojin sun daƙile yunƙurin sace mutane a garin Zaki-Biam da ke ƙaramar hukumar Zaki-Biam na jihar Benue, inda yayin musayar wuta sojojin suka kashe wani mai garkuwa da mutane tare da ƙwace ƙaramar bindiga da kuma tarin alburusai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here