Shugabannin bankuna na amsa tambayoyi kan badakalar Betta Edu da Sadiya – EFCC

0
160
Sadiya Faruq, Betta Edu

Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta ce tana bincikar shugabannin bankuna da aka gano hannunsu a badaƙalar kudaden ma’aikatar jinƙai da ta sa aka dakatar da Betta Edu daga matsayinta na minista.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce, a halin yanzu, “ana gudanar da bincike kan bankuna da ke alaka da badaƙalar

“Manajan daraktan bankunan sun ba da muhimman bayanai game da badakalar,” wadda kawo yanzu ita ce mafi daukar hankali a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Oyewale ta kara da cewa hukumar EFCC taa kwato karin kimanin Naira miliyan 534 kimanin Dala 445,000 abinciken da take wa dakatacciyar ministar agaji, Beta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar Farouq.

Hukumar ta bayyana a cewa har yanzu babu wanda ta wanke cikin Sadiya ko Beta Edu da sauran jami’an ma’aikatar daga zargin almundhanar da suke fuskanta.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce Dala 445,000 da kuma Naira biliyan 32.7 da hukumar ta kwato daga matan biyu wani ɓangare ne na kudaden tallafin da Gwamnatin Tarayya ta ba wa ma’aikatarsu domin rage raɗaɗin talauci a tsakanin ’yan Najeriya.

A cewarsa, kuɗaɗen sun hada na tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, da aka dawo wa Najeriya da su daga ƙasashen waje.

Sauran sun haɗa da kuɗaɗen tallafin COVID-19 da kuma rancen da Najeriya ta karɓo daga Bankin Duniya da aka ba wa ma’aikatar domin raba wa al’ummar ƙasa tallafin rage raɗaɗin talauci.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here