Najeriya ta buaci a kai zuciya nesa kan rikicin Iran da Isra’ila

0
168
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin Najeriya ta bi sahun sauran ƙasashe wajen yin kira da a kai zuciya nesa kan barazanar Iran da Isra’ila, yayin da ake ci gaba da tattaunawar diflomasiyya don ganin an kwantar da hankula da kuma kaucewa yaɗuwar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya. 

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar a ranar Lahadi, ta yi kira ga ƙasashen da su duba batun warware rikici cikin lumana, domin samar da zaman lafiya da kuma tsaro a duniya baki-ɗaya. 

Hakan na zuwa ne bayan da Iran ta kaddamar da hari kan Isra’ila a daren Asabar, inda ta ce harin na a matsayin ramuwa ne na kisan wasu kwamandojinta da Isra’ila ta yi a wani hari da ta kai karamin ofishin jakadancin ƙasar a Siriya, ranar 1 ga watan Afrilu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here