Dan sanda ya hallaka kansa a Maiduguri

0
207

Rahotanni daga Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno, sun bayyana cewar wani Sufeton dan sanda ya hallaka kansa har lahira a jihar.

Marigayin na aiki ne da ofishin ’yan sanda na Gwange a Borno.

Wasu majiyoyi daga yankin, sun bayyana cewar dan sandan na cikin koshin lafiia kwanaki uku da suka wuce.

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin da ya sa jami’in ya dauki wannan mummun mataki ba.

Amma wani makocinsa da ke Layin Baya a unguwar Wulari Jerusalem a Maiduguri ne, ya ja hankalin mutanen yayin da ya dan sandan ya dauki lokaci bai fito ba kuma wani wari na fitowa daga dakinsa.

Nan take aka kai rohoton faruwar lamarin hedikwatar rundunar ‘yan sandan Borno, inda aka aike jami’ai zuwa wajen da lamarin ya faru.

“A safiyar yau ne mutanen da ke gidan suka fara jin wani wari na fitowa daga dakinsa; kuma kofarsa a rufe ta ke ta baya.

“’Yan sanda sun zo kuma sun karya kofar dakin, inda suka iske gawarsa a kwance. A halin yanzu suna cikin gidan,” a cewar majiyar.

Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar game da faruwar lamarin.

Kazalika, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Kenneth Daso, bai amsa kiran da Aminiya ta yi masa ba.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here