Kotu ta aike da Bobrisky gidan maza har na tsawon wata 6

0
217

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta ɗaure Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky a gidan yari ba tare da wani zaɓin biyan tara ba.

Mai shari’a Abimbola Awogboro ya yanke wa Bobrisky hukuncin watanni shida, wanda ke tsare tun bayan kama shi a makon jiya.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC dai ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume shida.

An yi watsi da tuhume-tuhume biyu, yayin da ya amsa laifin cin zarafin Naira, amma ya nemi a yi masa afuwa a matsayinsa na wanda ya fara aikata laifi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here