Yanzu-yanzu: Ba a ga watan Karamar Sallah a kasar Saudiyya ba

0
213

Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun tabbatar da cewa ba a sami ganin jinjirin watan Shawwal ba wato watan karamar Sallah.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sahihin shafin Haramain sharifain na Kasar ya fitar yau litinin.

Masu ganin watan sun ce sun kasa ganin jinjirin watan na Shawwal sakamakon yanayi gajimare da hadari da aka yini da shi a wasu sassa na kasar kamar Riyadh da Tumair da Sudair.

Idan za’a iya tunawa tun da sanyin safiyar wannan rana ta litinin kadaura24 ta rawaito masana ilimin taurari a kasar dama sun yi hasashen ba lallai a ga jinjirin watan na Shawwal ba saboda Chanji yanayi.

Hakan dai na tabbatar da cewa al’ummar musulmi dake ƙasar Saudiyya zasu gudanar da azumi talatin (30) a bana , kuma hakan ya nuna cewa za’a yi idin karamar Sallah na bana ne a kasar a ranar Laraba 10 ga watan afirilu 2024.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here