Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun karamar sallah

0
218
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Talata da Laraba 9 da 10 ga Afrilu, 2024 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Sallah karama.

Kadaura24 ta rawaito Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar, Aishetu Ndayako ya fitar ranar Lahadi.

Ministan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan mai alfarma lafiya.

Tunji-Ojo ya yi kira gare su da su yi koyi da kyawawan dabi’u da halaye na kyautatawa, soyayya, hakuri, zaman lafiya, tausayi, irin na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi misali da shi.

Ministan na yiwa daukacin al’ummar musulmi barka da Sallah tare da addu’ar Allah ya karɓi ibadun da al’ummar musulmi suka yi a cikin watan na azumin Ramadan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here