Sojoji sun hallaka ‘yan bindiga 3 a Kaduna

0
182

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga guda uku a wani samame a jihar Kaduna

Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce ta samu nasarar kashe ‘yan bindigar ne bayan samun bayanan sirri kan wajen da suke zama, inda suka yi musu kwantan ɓauna tare da kashe su. 

Dakarun sojin sun ce sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar kafin kashe uku daga cikinsu yayin samame da suka kai kauyen Kidandan na karamar hukumar Giwa ranar Juma’a. 

“Yan bindigar na kan hanyarsu ta zuwa gyara baburansu, wadanda suke amfani da su wajen aikata ta’addanci a jihar Kaduna da kuma fadin yankin arewa maso yamma kafin su gamu da ajalinsu,” in ji sanarwar sojojin.

Sun kuma kwato makamai da suka hada da bindigar Ak-47, harsasai, babura hudu da kuma wani akwatin radio guda ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here