Gwamnatin tarayya na shirin fito da sabon katin dan-kasa mai hade da katin banki

1
212

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da wani sabon tsari na ƙaddamar da sabon katin ɗan-ƙasa wanda ya sha bamban da wanda ake da shi a halin yanzu.

Gwamnatin Nijeriyar tare da haɗin gwiwar Hukumar da ke Kula da Shaidar Zama Dan-Kasa NIMC da Babban Bankin Nijeriya CBN da Shirin Kula da Hada-hadar Kuɗaɗe Tsakanin Bankuna NIBSS ne suka fito da wannan sabon tsarin wanda zai haɗe katin ɗan-ƙasa da na banki wuri guda.

A cikin wata sanarwa da hukumar NIMC ta fitar, ta ce za a iya amfani da katin domin abubuwa da dama waɗanda suka haɗa da amfani da shi wurin morar ababen more rayuwa na gwamnati da kuma haɗa shi da asusun banki domin iya cire kuɗi da shi.

Haka kuma gwamnatin ta ce ƴan Nijeriyar za su iya amfani da sabon katin domin samun tallafin irin daban-daban da gwamnatin ƙasar ke bayarwa.

Gwamnatin ta ce za a iya amfani da katin wurin sufuri da inshorar lafiya da samun bashi da samun tallafin makamashi.

Sai dai gwamnatin ta ce ƴan Nijeriya masu shaidar NIN ne kaɗai za su samu wannan katin.

Hukumar ta NIMC ta ce za ta ci gaba da bin doka domin tabbatar da kiyayewa tare da kare bayanan jama’a waɗanda ke a hannunta.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here