Yadda aka ninka farashin wutar lantarki a Najeriya

0
225

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince da karin kudin wutan lantarki ga kwastomomin da ke karkashin rukunin samun wuta na Band A.

A wani taron manema labarai a wannan Larabar a Abuja, mataimakin shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce karin kuɗin zai mayar da kuɗin ma’aunin wutar lantarki na kilowatt ɗaya duk sa’a daga Naira 66 da ake biya a yanzu zuwa Naira 225.

Mun gano cewa waɗanda ke karkashin tsarin Band A ne ke samun wutar lantarkin na sa’o’i 20 a kullum.

Oseni ya ce wadannan kwastomomi suna wakiltar kashi 15 cikin dari na masu amfani da wutar lantarki miliyan 12 a kasar.

Ya kara da cewa hukumar ta sauke wasu kwastomomin da ke kan tsarin samun wuta daga Band A zuwa Band B.

Wannan ya zama wajibi ne saboda rashin cika sa’o’in da ake bukata na wutar lantarki da kamfanin rarraba wutar lantarkin ke samarwa.

“A halin yanzu muna da fidoji 800 da aka kasafta a matsayin Band A, amma yanzu za a rage su zuwa kasa da 500.

A baya dai Kamfanin Dillancin Labarai na Bloomberg ya ce za a ba kamfanonin wutar lantarki damar kara farashin wutar lantarki zuwa N200 ($0.15) a kowace kilowatt daga naira 68 ga masu amfani da wuta a birane daga wannan watan.

Bloomberg ya bayyana hakan ne a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ruwaito cewa, gwamnati ta ce waÉ—annan kwastomomi su ne masu wakiltar kashi 15% na al’ummar kasar da ke  amfani da kashi 40% na wutar lantarkin da ake samarwa.

WaÉ—ansu majiyoyi daga fadar shugaban kasa da ke da masaniya kan lamarin sun ce za ayi hakan ne da nufin janyo hankulan sabbin masu zuba jari a harkokin wutar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here