Matatar man Dangote ta fara sayar da mai ga ‘yan kasuwa

0
217
Aliko-Dangote
Aliko-Dangote

Matatar man hamshakin attajirin Najeriya Aliko Dangote ta fara fitar da albarkatun man fetur din da ta tace, kamar yadda daya daga cikin manyan jami’an kula da matatar da kuma kungiyar dillalan man fetur din a Najeriya suka tabbatar.

Daya daga cikin manyan jami’ai a rukunonin kamfanin na Dangote Devakumar Edwin ne ya tabbatar da samun wannan ci gaba, yayin zantawa kamfanin dillancin labarai na Reuters, inda ya ce tuni suka fara rarraba wa ‘yan kasuwa man disel da kuma man jiragen sama.

A cewar jami’in, litar mai miliyan 37 suke fatan cimma fara dorawa manyan jiragen ruwa, amma a halin yanzu suna iya lodin litar man miliyan 26.

Kamfanin dillancin labaran na Reuters ya kuma ruwaito shugaban kungiyar dillalan man fetur na Najeriya Abubakar Maigandi na cewa, sun cimma matsayar sayen litar man disel daga matatar man ta Dangote kan farashin naira dubu 1,225, kwatankwacin kusan dalar Amurka guda, wanda za su rarraba zuwa sassan Najeriya.

Matatar man ta Dangote da ke jihar Legas ta lakume dalar Amurka biliyan 20 kafin kammala aikin gininta, wadda za ta rika tace gangar danyen mai dubu 650,000 a kowace rana, abinda yasa idan har ta fara cikakken aikin da aka tsara mata a bana ko kuma badi, matatar za ta zama mafi girma a nahiyar Afirka da ma Turai, ci gaban da ake fatan zai kawo karshe ko kuma rage dogaron da Najeriya ke yi wajen shigar da tataccen man fetur daga Turai, duk da dimbin arzikin danyen man da take da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here