Madrid ta kara wa Barcelona tazarar maki a saman taburin La liga

0
308

Real Madrid ta bada tazarar maki takwas a saman taburin La liga gaban Barcelona, bayan doke Athletico Bilbo da ci 2 – 0 a wasan da suka fafata daren jiya a gida, da taimakon kwallaye biyu masu kyau daga Rodrygo.

Wannan dai itace wasan karshe da Real Madrid ta doka gabanin karawar da za ta yi da Manchester City a gasar zakarun Turai.

Dan wasan gaban na Brazil ya fara zura kwallo a raga da tazarar yadi na 20, mintuna 8 da soma wasa, kafin ya kara na biyu bayan hutun rabin lokaci a mintuna na 73.

Real Madrid, wadda ta yi bakwancin dan wasan tsakiyar Ingila Jude Bellingham da dawo bayan dakatarwa, ta hada maki 75 saman teburi gaban Barcelona mai maki 67 da kwanten wasanni takwas.

Athletic Bilbao, wacce za ta kara da Mallorca a wasan karshe na gasar cin kofin Copa del Rey a Seville ranar Asabar, sun kasance na hudu da maki daya tsakaninta da Atletico Madrid mai matsayi na biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here