‘Yan sanda sun kama wani malami da sassan jikin dan’adam a Ondo

0
179

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ondo ta ce ta kama wani malami da ake kira da Oluwafemi Idris kan zargin mallakar sassan jikin ɗan’adam.

Kwamishinan ‘yansandan jihar Abayomi Oladipo ya ce hukumarsu ta samu rahoton daga wata majiya mai ƙarfi a farkon watan Janairun 2024.

Idris dai an fi saninsa da “Alfa” a yankin da yake zaune, kuma yana ajiye sassan jikin mutane a gidansa da manufar amfani da su wajen harkokin addini.

Ya ce daga nan ne ‘yansanda suka dauki mataki suna kama wanda ake zargi, inda suka kama shi da hannun mutum da koda kuda uku da zuciya da ƙashin baya da kuma harshe lokacin da suke bincike a gidansa da ke Akoko.

“Wanda ake zargin ya yi iƙirarin shi malamin addinin musulunci ne, kuma wani abokinsa ne ke kawo masa sassan jikin wanda shi ma malami ne, akwai wani Samuel Ketule da shi ma yake kawo masa, sai Babatunde Kayode da ya kawo masa kawunan mutum uku,” in ji Kwamishinan ‘yansandan.

“Babatunde da Olawo duka sun shiga hannu. Kuma ana ta kokarin yadda za a kama ɗaya malamin da shi ya amba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here