Ina tare da gwamnatin Tinubu – Buhari 

0
188

Tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce yana yi wa gwamnatin Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC fatan samun nasara a ragama da suka karɓa na jagorantar ƙasar.

Buhari ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da shugaba Tinubu ta wayar tarho a ranar Juma’a domin taya shi murnar cika shekara 72 da haihuwa.

Wata sanarwa da tsohon maitaimakawa tsohon shugaban kan harkar yaɗa labarai, Garba Shehu ya fitar, ta ce Buhari na addu’ar ganin jam’iyyarsu ta APC da kuma gwamnatin da ta gaje sa ta samu nasarori da suka kamata.

“Yi wa shugabanni addu’a abu ne mai kyau, saboda samun nasararsa ba ga shi kaɗai bane, amma ga ƙasa baki-ɗaya,” in ji Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here