Tinubu ya bukaci malaman addini su daina la’antar Najeriya a wa’azinsu

0
194

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kira ga malamai da shugabannin addini da su guji “ƙasƙantarwa da kuma la’antar ƙasar” a cikin wa’azi kuma huɗubobinsu.

Tinubu ya yi kiran ne ranar Alhamis yayin da yake buɗe-baki tare da sarakuna da kuma jagororin addinin Musulunci da na Kirista a fadar shugaban ƙasa, yana mai jaddada cewa wa’azin da suke yi yana da matuƙar tasiri a cigaban ƙasar.

“Kishin ƙasar nan yana hannunku. Ku yi mata addu’a, ku ilimantar da yaranmu. Huɗubar da muke yi a masallatai da coci-coci na da matuƙar muhimmanci,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Kada ku la’anci ƙasarku…Idan shugaba ba mutumin kirki ba ne ku bari zaɓe ya zo ku sauya shi, amma kada ku la’anci ƙasar. Da ma an tsara shugabanci ne da nufin kawo sauyi.”

Sarkin Zazzau Nuhu Bamalli ne ya wakilci Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III a taron, wanda ya samu halartar Sakataren Ƙungiyar Kiristoci ta CAN Samson Fatokun.

Shi ma Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya nemi malaman da su “dinga haɗa kan al’umma don guje wa rikicin ƙabilanci da na addini”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here