Tinubu ya bai wa iyalan sojojin da aka kashe tallafi

0
194
Tinubu
Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin kyautar gidaje da kuma tallafin karatu ga iyalan sojojin da aka kashe a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris.

Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a yayin jana;izar sojojin, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta kyale iyalan waɗannan mutane su walaƙanta ba.

“Mutane ne da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen kare ƙasarsu, domin haka ba za mu bari su walaƙanta ba.

“Gwamnati ta bai wa iyalansu gidajen zama da kuma tallafin karatu ga ya’yansu da suk mutu suka bari.

“Za mu tabbatar sun amfana da duk wani tallafi da iyalan waɗanda suka rasa rayuwarsu suke samu a hukumance,” in ji Tinubu.

Tinubu ya umarci ma’aikatar fanso ta ƙasar da ta kammala biyan hakkin iyalan mamatan nan da kwana 90.

An bai wa iyalan mamatan lambar girma da kuma shaida a yayin taron jana’izar tasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here