Janar Tiani ya tattauna da Putin kan haɗin gwiwar tsaro 

0
218

Shugaban mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya tattauna ta wayar tarho a ranar Talata da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin game da “ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro”, a cewar sanarwar da aka fitar a hukumance. 

Tuni dai ƙasashen biyu suka amince a watan Janairu domin ƙarfafa alaƙar soji a lokacin da Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine ya jagoranci wata tawaga zuwa birnin Moscow. 

Nijar ta kasance kan gaba a haɗin gwiwa da Ƙasashen Yammacin Duniya wajen yaƙar masu tayar da ƙayar-baya a yankin Sahel, amma ta rungumi Rasha a matsayin sabuwar abokiyar tsaro tun bayan hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a bara. 

Shugabanin ƙasashen biyu “sun yi magana kan buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin tsaro…domin shawo kan barazanar da ake fuskanta a halin yanzu,” in ji sanarwar ta Nijar, wadda aka karanta a gidan rediyon gwamnatin ƙasar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here