Gwamnantin Kano zata cika wa maniyyatan jihar naira dubu 500

0
211

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da amincewa da tallafin naira dubu 500 ga maniyyata hajjin bana da suka fito daga jihar, a wani yunƙuri na rage masu raɗaɗin ƙarin kuɗin kujerar hajji da hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta yi.

A baya-bayan nan ne hukumar alhazan ta najeriya ta sanar da ƙara kuɗin kujerar hajjin da kusan naira miliyan biyu sai dai ta bayyana cewa ƙarin bai shafi maniyyatan da ke ƙarƙashin tsarin adashin gata ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na X. 

A yanzu duk maniyyaci daga jihar Kano wanda ba ya tsarin adashin gata, zai yi ƙarin naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a maimakon sama da naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara.

Ya ce “duk maniyyacin da ya yi rajista kuma ya biya kafin alÆ™alamin naira miliyan 4.7 da naira miliyan 4.5 a hukumar alhazai ta jiha a yanzu zai biya naira miliyan 1.4 a maimakon naira miliyan 1.9.”

To sai dai sanarwar gwamnan ba ta fayyace ko tallafin zai kasance ga dukkannin maniyyatan jihar ba ne ko kuma wadanda ba za su iya yin cikon ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here