Sall ya taya Bassirou murnar lashe zaɓen shugaban kasar Senegal 

0
188

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya taya ɗan takarar jam’iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi, 24 ga watan Maris. 

“Ina yabawa game da yadda aka yi zaɓen shugaban ƙasa na  ranar 24 ga watan Maris, 2024 ba tare da matsala ba kuma ina taya murna ga wanda ya yi nasara, Mr. Bassirou Diomaye Faye, wanda alamu suka nuna cewa shi zai yi nasara. Wannan nasara ce da dimokuraɗiyyar Senegal,” in ji Sall a sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin. 

Sall ya fitar da saƙon ne jim kaɗan bayan tsohon Firaministan Senegal kuma ɗan takarar gamayyar jam’iyyu masu mulki ya amsa shan kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa.

Amadou Ba, ɗan takarar jam’iyya mai mulki ya faɗa a wata sanarwa daga ofishin kamfe ɗinsa ranar Litinin, cewa yana taya murna ga ɗan takarar jam’iyyar adawa, Bassirou Diomaye Diakhar Faye, kuma yana yi masa fatan alheri.

Sakamakon farko ya nuna cewa Faye ya samu aƙalla kashi 57 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Ba ya samu kashi 31. 

Nasarar da ya samu a zagayen farko na zaɓen ta dace da abin da aka gani na yadda mutanen ƙasar ke nuna ɓacin-ransu da rashin aikin-yi da shugabanci nagari a ƙasar da ke Yammacin Afirka.

Diomaye Faye, wanda ke da goyon baya daga shahararren ɗan adawa Ousmane Sonko, ya sha alwashin raba Senegal da rashawa a ɓangaren gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here