An gudanar da zanga-zangar neman tumbuke Netanyahu

0
164

Al’umar Isra’ila sun gudanar da zanga-zangar neman yin waje da Firaministan kasar saboda illar dake akwai ta ci gaba da yakin Gaza.

An fuskanci wata takaddama a tsakanin masu zanga-zanga da jami’na ‘yansanda a Tel Aviv babban birnin Isra’ila a dai dai lokacin da ake ci gaba da fafata yaki a Gaza.

‘Yan sandan Isra’ila sun tsare wani mutum a yayin wata zanga-zangar neman sabon zabe, tare da nuna takaicin gazawar gwamnatin kasar wajen kubutar da daukacin mutanen da ke garkame a zirin Gaza.

Hakanan a wani bangare kuma ‘Yan sandan sun kakkama wasu masu zanga-zanga a birnin Tel Aviv, wadanda suka yi kira da firaminista Benjamin Netanyahu ya yi murabus da kuma gudanar da zabe da wuri a yayin da Isra’ila ke ci gaba da barin wuta a Gaza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here