Sojoji sun kubutar da almajirai 16 da aka sace a Sokoto

0
180

Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadarin Daji sun kuɓuta da ɗaliban tsangaya 16 da wata mata guda waɗanda ƴanbindiga suka sace ranar 9 ga watan Maris a karamar hukumar Gada na jihar Sokoto.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na shelkwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, a yau Asabar.

Buba ya ce an samu nasarar kuɓutar da almajiran ne ranar Alhamis a wani aikin haɗin gwiwa tsakanin sojoji da kuma wasu jami’an tsaro a faɗin ƙasar.

Ya ce tuni aka miƙa ɗaliban zuwa ga hannun gwamnatin jihar Sokoto domin hannanta su ga iyayensu.

Manjo-Janar Edward ya ce sojojin na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace waɗanda ba su aikata laifin komai ba.

Da yake tarban almajiran, Gwamna Ahmad Aliyu, ya yaba wa sojoji da kuma ofishin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro da irin ƙoƙari da suka yi wajen kuɓutar da ɗaliban.

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labaru ga gwamnan Abubakar Bawa ya fitar, ta ce an kuma duba lafiyar dukkan ɗaliban domin tabbatar da koshin lafiyarsu.

“Dukkan ɗaliban sun kasance cikin koshin lafiya kuma za mu miƙa su ga iyayensu,” in ji gwamnan.

Ya kuma sanar da tallafin buhun hatsi biyu da naira 100,000 ga kowane almajiri.

Gwamna Aliyu ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Sokoto da su ci gaba da bai wa gwamnatinsa goyon baya, a ƙoƙarinta na sama da tsaro a faɗin jihar.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here