‘Ina iya mutuwa a hannun jami’an DSS’ – Nnamdi Kanu

0
181

Jagoran ƙungiyar ƴan awaren Biyafara masu neman ɓallewa daga Najeriya, Nnamdi Kanu ya koka kan halin da yake ciki a hannun jami’an hukumar tsaro ta farin kaya – DSS.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana gaban babbar kotu a ranar Talata domin ci gaba da sauraron ƙararsa kan tuhumar cin amanar ƙasa da ta’addanci.

Ana yi masa tuhume-tuhumen ne da suka shafi tayar da husuma da kuma cin amanar ƙasa sanadiyyar gwagwarmayar da ƙungiyarsa ke yi a gabashin Najeriya na ganin ta zama ƙasa mai cin gashin kanta.

A harabar kotun, Kanu ya ɗage rigarsa domin nuna cewa ba a bashi kulawar da ta kamata inda ya yi iƙirarin cewa “zan mutu a hannun DSS.”

Shugaban na Ipob ya nuna wani ɓangare na jikinsa da ke da tabo bayan da kotu ta ba shi damar magana game da buƙatarsa ta neman beli da kotun ta yi watsi da ita.

Kanu ya ce ya na fama da matsalar ciwon zuciya sai dai magugunan da ake ba shi a hannun DSS “ba su da amfani”.

Ya ƙara da cewa DSS ba ta ba shi damar ganin likitan da yake so ba.

“Zan mutu a hannun DSS kuma suna ba ni magani mara tasiri. Suna duba ni game da matsalar zuciya amma maganin da suke ba ni ba shi da amfani. Suna son na mutu a tsare,” in ji Nnamdi Kanu.

Jagoran na Ipob ya buƙaci kotun ta mayar da shi gidan gyaran hali na Kuje sai dai mai shari’a Nyako ta ce tana da ikon ajiye Kanu duk inda ta ga babu barazanar tsaro.

Mai shari’a Nyako ta nemi a ci gaba da tsare Kanu a hannun DSS.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here