Gobara ta tashi a sansanin yan gudun hijira a Maiduguri

0
214
Borno
Borno

Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Garkin Block da ke Maiduguri a Jihar Borno.

A cewar wani ganau, gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Litinin.

Ya ce, cikin kankanin lokaci wutar ta bazu cikin sansanin, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna yankin.

Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) ta ɗauki mataki kan lamarin, inda jami’an kashe gobara suka isa da misalin ƙarfe 5:25 na yamma domin kashe gobarar.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a iya tantance girman barnar da gobarar ta yi ba, haka kuma, ba gano musabbabin tashin gobarar ba daga bangarorin da abin ya shafa ba.

Aminiya ta ruwaito cewa, sansanin ’yan gudun hijira na Garkin Block na nan a kan hanyar Madinatu da ke cikin birnin Maiduguri.

AMINIYA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here