Gwamnatin Nijar ta soke yarjejeniyar soji da Amurka

0
172

Gwamnatin mulkin soji ta Nijar karkashin Janar Abdourahamane Tchiani ta ce ta soke yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka.

Hukumomin sojin sun sanar da haka ne, bayan da a baya suka yanke irin wannan alaka da Faransa, har ma ta kori dakarun tsohuwar uwar gijiyar tata ta mulkin mallaka da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin daga kasar.

Tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki ne a ranar 26 ga watan Yuli na shekarar da ta gabata suke daukar irin wannan mataki na yanke hulda da kasashen yamma, tare da kulla dangantakar tsaro da Rasha.

Amurka da Nijar suna da yarjejeniyar soji tun 2013, wadda a karkashinta dakarun Amurka da ke hamada suke amfani da kananan jiragen sama marassa matuka wajen yakar kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.

To amma a watan Yuli na shekarar da ta gabata sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum, abin da ya sa kuma gwamnatin Amurka ta katse taimakon kudi da take bai wa kasar ta yankin Afirka ta Yamma.

A farkon makon nan ne wata tawaga daga Amurka ta je Nijar din da zummar mayar da tattaunawa a tsakaninsu.

Maimakon a samu hakan sai , kakakin gwamnatin sojin ya bayyana a tashar talabijin ta kasar ta Nijar, yana zargin tawagar ta Amurka da saba ka’ida ta hanyar zuwa ba tare da wata sanarwa ta gargadi ba.

Daga nan kakakin sojin Kanar Amadou Abdramane ya ce an ma soke yarjejeniyar gaba daya.

Tun a baya sojojin da suka yi juyin mulkin sun janye jakadunsu daga kasashen Faransa da Amurka da Najeriya da kuma Togo.

Juyin mulkin na Nijar ya kasance daya daga cikin guda takwas da sojoji suka yi a yankin Afirka ta yamma da kuma Afirka ta tsakiya.

Sauran Æ™asashen da sojoji suka yi juyin mulkin bayan Nijar su ne Burkina Faso, da Mali, da Guinea da kuma Chadi, kodayake ita Chadi É—an marigayi shugaban Æ™asar ne ya karÉ“e iko bayan kashe mahaifinsa Idriss debby a fagen yaÆ™i da ‘yan tawaye.

Juyin mulkin ya sa kungiyar kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS sanya wa Nijar takunkumin kudi da na kasuwanci.

Bayan wani lokaci kuma kasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, suka bayyana ficewa daga kungiyar ta Yammacin Afirka.

Daga baya-bayan nan ne kuma kungiyar kasashen ta janye dukkanin takunkumin da ta sanya wa Nijar din tare da bayar da umarni da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya yi na bude iyakokin kasarsa da Nijar din.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here