Legas za ta bude kasuwannin sayar da abinci a farashi mai rahusa

0
162
Kayan Abinci

Gwamnatin jihar Legas za ta buɗe kasuwannin sayar da abinci a faɗin jihar.

Kauwannin za su riƙa sayar da kayan abincin a cikin farashin mai rahusa.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Gbenga Omotoso, shi ya bayyana cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.

Ire-iren abincin da za a sayar da ɗin sun haɗa da shinkafa, wake, gari, burodi, kwai, tumatir da kuma borkono, inda Gbenga ya ce za a yi ragin kashi 25.

“Domin tabbatar da cewa kayan abincin ya kai ga illahirin ƴan jihar Legas da kuma kaucewa ɓata-gari shiga ciki, za a ɓullo da wani tsari na bayar da tikiti domin sanin duk waɗanda suka saya,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma ce an zaɓi masu harkar abinci na musamman domin gudanar da shirin.

“Za a riƙa sayar da buhun shinkafa mai nauyin kilogram biyar kan N5,325 yayin da mai nauyin kilogram ɗaya kuma za a sayar kan N1,065, buhun wake mai kilogram biyar N6,225 yayin da mai nauyin kilogram ɗaya kuma N1,245. Za mu sanar da farashin sauran kayan abincin su ma yayin buɗe kasuwannin,” in ji Gbenga.

Ya ce za a buɗe kasuwannin ne a wurare 27 a Ikeja, shida a Legas Island, tara a Ikorodu, biyar a Epe, sai kuma goma a yankin Badagry.

BBC

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here