An hallaka sojojin Nijar 12 a wani harin kwanton-bauna a Tillaberi

0
226
Tillaberi-Nijar
Tillaberi-Nijar

Ana zargin masu ikirarin jihadin sun kashe sojojin Nijar 12 a kudu maso yammacin yankin Tillaberi, kamar yadda gidan talabijin na kasar ya ruwaito.

An kai harin ne kan sojojin da ke gadin fadar shugaban kasa da ke yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a yayin wani samame da suka kai ranar Lahadi da yamma a garin Anzourou, a cewar gidan talabijin na Tele Sahel.

“Martanin da dakarun sojin suka mayar ya jawo asarar rayuka sosai a gwabzawar,” in ji gidan talabijin din.

Hakan na faruwa ne kasa da mako guda da kai harin kwanton bauna yankin Tillaberi, inda aka kashe sojojijn Nijar 17, sakamakon wani hari da shi ma ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai shi kan iyakar Mali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here