Yadda masu zanga-zanga suka isa gidan gwamnatin Kano duk da gargadin jami’an tsaro

0
214
Zanga-Zanga
Zanga-Zanga

Tun farko da safiyar yau ne shugabancin jam’iyyun NNPP da APC suka bukaci mambobin su da su kwarara kan titi da nufin gudanar da zanga-zangar lumana game da jita-jitar baiwa kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar cin hanci don ta sauya akalar sakamakon zaben.

Sai dai kuma tun da sanyin Safiyar yau ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Muhammed Usaini Gumel ya fitar da sanarwar gargadi da kuma haramta duk wata zanga-zanga don tabbatar da doka da oda.

Bayanai sun ce tuni daruruwan mutanen suka mikawa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf takardar koken su tare da bukatar ya mikata ga shugaban kasa da nufin sanya idanu da kuma tabbatar da ganin an bar gaskiya ta yi halin ta a shari’ar da ake ci gaba da yi.

Masu zanga-zangar sun sami tarbar gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, inda kuma ya yi musu alkawarin mika takardar ga shugaban kasar, tare da nuna kwarin gwiwar cewa a matsayin shuga Tinubu na dattijo zai yiabinda ya dace a game da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here