Somaliya ta haramta amfani da manhajar TikTok a kasar

0
149
TikTok
TikTok

Somaliya ta dakatar da kafofin dandalin sada zumunta na TikTok da Telegram, tare da shafin caca na 1XBet.

Dalilin da ya sa gwamnatin kasar ta dauki wannan mataki shi ne ikirarin cewa “kungiyoyin ‘yan ta’adda da kungiyoyin da ke da hannu wajen yada abubuwan da ba su dace ba” suna amfani da wadannan kafafen yada labarai ne wajen yaudarar jama’a.

Wannan ya zo ne daidai lokacin da Somaliyya ta bayyana kudurinta na fatattakar mayaƙan al-Shabab, wadanda ke ci gaba da rike madafun iko a wasu sassa na kasar da kuma burin cimma wannan gagarumin buri a cikin watanni biyar masu zuwa.

Ma’aikatar sadarwa da fasaha ta Æ™asar ta umarci kamfanoni masu samar da intanet da su aiwatar da dokar kafin ranar 24 ga watan Agusta inda suka ce rashin yin biyayya zai iya haifar da matakin shari’a da ba a fayyace ba.

A yayin wani taro na baya-bayan nan kan harkokin tsaro na intanet da na sada zumunta da aka gudanar a birnin Mogadishu, babban birnin kasar, an yi nuni da irin illar da shafukan intanet ke yi wa matasa kuma sun taimaka wajen asarar rayuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here