Kalubalen da ake fuskanta a Najeriya na wucin gadi ne – Tinubu

0
199

A ranar Alhamis din ta gabata ne Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa kalubalen da ake ci gaba da fuskanta a kasar nan na wucin gadi ne.

Tunibu ya bayyana haka ne a taron da aka gabatar abirin tarayya Abuja ranar Alhamis inda aka gudanar da wallafa littafin Brutaly Frank wanda tsohon ministan yada labarai Edwan Clark ya rubuta.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kara da cewa Najeriya na da matukar sarka-kiya amma hakan bazai zama wani abun damuwa ba wajen gudanar da ita yadda ya dace kuma bazatai wahalar sarrafawa ba.

Sanata Jodge Akume ya ce idan ana so wannan kasar ta zauna lafiya abu guda daya za a yi, domin samun ci gaba da tabbatuwar zaman lafiya a kasar nan.

Shugaban yace radadin da mutanen kasar nan ke fama da shi dole ne sai an yi yunkurin kawar da shi na din-din-din.

Shugaban ya kuma cewa radadin da al’umma ke fama da shi na cire tallafin mai na wucin gadi ne domin wannan tsarin ba wai an saka shi bane don hakan ya dore ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here