Manyan matakai 5 na rage raɗaɗi da gwamnatin tarayya ta shirya za ta ɗauka

0
186

Majalisar kula da Tattalin Arziƙi a Najeriya ta sanar da wasu sabbin matakai da gwamnati za ta ɗauka don samar wa ‘yan ƙasar sauƙin rayuwa sanadin wahalhalun janye tallafin man fetur.

Majalisar ta sanar da matakan ne a ƙarshen taron wata-wata da ta yi a ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima.

Hakan na zuwa ne bayan da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jingine batun raba kuɗin tallafi na naira 8,000 ga gidajen talakawa miliyan 12 a faɗin ƙasar na tsawon wata shida.

Jingine batun tallafin na naira 8,000 ya biyo bayan sukar shirin da al’umma suka yi, bayan amincewa da yin hakan da shugaban ya samu daga Majalisar Dokokin ƙasar.

Taron da Majalisar Tattalin Arziƙi ta Najeriyar ta gudanar a ranar Alhamis, wanda shi ne na biyu bayan kama aikin sabuwar gwamnatin ya fi mayar da hankali ne a kan batutuwa guda biyu da suka fi tasiri wajen jefa ‘yan ƙasar cikin mawuyacin hali:

Bayan kammala taron, an amince da ɗaukar wasu matakai na gaggawa domin tsamo ƴan Najeriya musamman mafiya rauni daga cikin halin da suka shiga.

Raba abinci da takin zamani

...

Mataki na farko da gwamnatin ta ce za ta ɗauka shi ne fitar da abinci daga rumbunan ƙasar domin raba wa al’umma.

A cewar bayanin gwamnatin jihohi za su raba abincin ne kan farashi daidai da na hukumar agajin gaggawa ta NEMA.

Baya ga wannan, za kuma a raba takin zamani ga manoma, don tallafawa wajen bunƙasa harkokin noma, domin samar da wadataccen abinci ga al’ummar ƙasar.

Raba kuɗin tallafi

Taron ya bayar da umarnin cewa kowace jiha ta tsara yadda za ta samar wa jama’arta sauƙi, ko dai ta hanyar raba tallafin kuɗi ko kuma ta hanyar da ta fi dacewa.

Haka nan an buƙaci jihohin su yi amfani da bayanai da suke da su na al’ummarsu da ke cikin talauci a maimakon bayanan da ake da shi na gwamnatin tarayya.

Ƙarin alawus kan albashin ma’aikata da yan fansho

Haka ma an amince da bai wa ma’aikatan gwamnati tallafin kuɗi a kan albashinsu har zuwa tsawon wata shida, sannan kowacce jiha ta tabbatar ta biya ma’aikata da ‘yan fansho dukkan basukan da suke bi.

Waɗannan in ji majalisar za a aiwatar da su ne ta hanyar amfani da rarar kuɗin da gwamnati za ta samu saboda janye tallafin man fetur da kuma daidaita harkar canjin kuɗi.

Samar da motocin sufuri

...

Taron ya kuma amince da samar da motocin bas-bas waɗanda za su taimaka wa harkokin sufuri a faɗin ƙasar.

Motocin za su kasance masu amfani da lantarki, inda gwamnati za ta samar da wuraren cajin motocin a wurare daban-daban.

Sufuri na daga cikin ɓangaren da lamarin cire tallafin man fetur ya shafa, inda farashin tafiye-tafiye ya yi tashin gwauron-zabi tun bayan janye tallafin na man fetur.

Bayanai na cewa da dama daga cikin al’mma a Najeriya sun jingine ababen hawa, wasu kuma sun rage tafiye-tafiye saboda tsadar kuɗin mota.

Maye gurbin man fetur da man CNG

Bugu da ƙari, taron ya amince da aiwatar da wani tsari na sauya makamashin da ababen hawa suka fi amfani da su daga man fetur wanda ya yi tsada yanzu zuwa wani nau’in iskar gas da ake kira CNG a taƙaice wanda Najeriya ke da shi mai tarin yawa kuma ga arha.

Jihohin ƙasar sun amince za su fara juya motocin jigilar ma’aikata zuwa masu amfani da iskar gas.

A ƙarshen watan Mayu ne shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ƙasar.

Lamarin ya haifar da ƙaruwar farashin man a faɗin ƙasar, wani abu da ya haifar da tashin farashin kayan masarufi.

Bugu da ƙari an ci gaba da fuskantar faɗuwar darajar naira bayan da babban bankin ƙasar ya sauya fasalin yadda yake tafiyar da lamurran kuɗi na ƙasar.

Tsadar rayuwa da wahalhalu da al’umma suka faɗa ciki sun janyo koke daga dukkanin ɓangarorin ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here