Sojojin ECOWAS sun shirya afkawa Nijar

0
184
Hafsoshin ECOWAS

Dakarun tsaron ECOWAS sun shirya fafatawa da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar idan aka kasa samun mafita ta hanyar diflomasiyya kan rikicin siyasar kasar, a cewar wani babban jami’i.

Kwamishinan ECOWAS kan Siyasa, Tsaro da Zaman Lafiya, Abdel-Fatau Musah, wanda ya bayyana hakan a taron da hafsoshin tsaron kungiyar ke yi a Ghana, ya zargi sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum da “yin wasan-buya” da kungiyar ta hanyar kin amincewa su gana da wakilanta.

“A shirye dakarun soji da na farin-kaya na Yammacin Afirka suke su amsa kiran yin aikinsu,” kamar yadda ya shaida wa taron dakarun tsaron kasashen kungiyar.

Ya jero rawar da ECOWAS ta taka a baya wajen aika dakaru kasashe irin su Gambia, Liberia da sauransu a matsayin wata hujja ta shirin da ta yi a yanzu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
“Idan ba a samu mafita ba za mu shiga Nijar tare da dakarunmu da kayan aikinmu don tabbatar da dawo da tsarin mulki. Idan sauran masu son dimokuradiyya za su goyi bayanmu muna maraba da hakan,” in ji shi.

Musah ya yi kakkausan suka kan sanarwar da sojojin Nijar suka fitar cewa za su tuhumi Mohamed Bazoum da laifin cin amanar kasa. Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai da ECOWAS duka sun nuna fargaba kan halin da yake ciki.

“Abin arashin shi ne mutumin da aka yi garkuwa da shi… shi ne ake tuhuma da laifin cin amanar kasa. Kowa ya san abin da ake nufi kan cin amanar kasar,” a cewar Musah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here