NNPC ya ciyo bashin dala biliyan uku cikin gaggawa

0
215

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Limited ya sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar ciyo bashin gaggawa daga bankin raya kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki na Afirka, wato AFREXIM Bank.

Bashin wanda ya kai dala biliyan uku, za a yi amfani da shi wajen biyan kudin danyen mai da ake bin kamfanin na NNPC bashi.

An sanya hannu kan yarjejeniyar bashin ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Laraba, kamar yadda NNPCL ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Bankin na AFREXIM zai samar da kudin nan-take don bai wa NNPC dama ta tallafawa tsarin gwamnatin tarayya kan hada-hadar kudi da haraji, da daidaita darajar Naira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here