Adadin albashin da Neymar zai dinga dauka a Saudiyya

0
255
Neymar
Neymar

Paris St-Germane ta amince da yarjejeniyar sayar da dan wasanta na gaba dan asalin Brazil wato Neymar ga Al-Hilal ta Saudiya a kan farashin euro miliyan 90, inda a yanzu zai rika karbar albashin euro miliyan 150 a Saudiyar, wato ninki shida na abin da PSG ke ba shi, kwatankwacin naira biliyan 126.


Sauya shekar dan wasan ta kuma kunshi cewa, zai kamala gwaje-gwajen lafiyarsa da kuma cike dukkanin takardun aiki.

Neymar wanda ya koma PSG a kan farashin euro miliyan 200 a shekarar 2017, ba ya cikin tawagar kungiyar da ta yi canjaras da Lorient a gasar Lig 1 a ranar Asabar.

Kazalika dan wasan ba ya cikin tsarin kocin kungiyar Luis Enrique a sabuwar kakar wasanni.

Bayanai na cewa Neymar na karbar albashin euro miliyan 25 a kowacce shekara a PSG ta Faransa, amma a yanzu zai rika karbar albashin euro miliyan 150 a kowacce shekara a Saudiya , wato ninki shida na abin da yake karba a PSG.

Neymar ya buga wa PSG jumullar wasanni 173, inda ya taimaka wa kungiyar lashe kofuna 13 da suka hada da kofin gasar Lig 1 guda biyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here