‘Yan ta’adda sun hallaka mutane 13 a jihar Borno

0
207
Borno
Borno

Rahotanni sun ce ‘yan ta’addan sun kai wannan harin ne a cikin talaitainin daren  Asabar zuwa wayewar garin Lahadi a kan wani sansani da ke Wulari, wani kauye da ke kusa da garin Konduga na jihar Borno.

Daya daga ciki jagororin ‘yan sa kai, Ibrahim Liman ya ce ‘yan ta’addan sun yi amfani da duhun dare da kuma na masara da ke gonakin da ake daf da yin girbi ne wajen kai wa sansanin farmaki.

Liman ya ce dakarun Najeriya sun tinkare ‘yan ta’addan, inda  aka yi mummunan ba-ta-kashi, lamarin da ya yi sandin mutuwar sojoji 3.

Wasu majiyoyi sun ce ko a yammacin Asabar, sai da ‘yan ta’adda suka yi wa wasu manoma kawanya a yayin da suke aiki a wata  gona, inda  suka kashe mutane 10 da ke aiki  a cikin gonar.

Kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun tsananta hare-hare a kan masu saran itace, manoma, masunta da ‘yan gwangwan, suna mai zarginsu da yi musu leken asiri.

Akalla mutane dubu 40 ne suka mutu sakamakon rikicin ‘yan ta’adda da aka shafe shekaru 14 ana yi  a Najeriya, rikicin da ya bazu zuwa makwaftanta Nijar, Kamaru da Chadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here