PSG ta dauki Dembele daga Barcelona

0
255

Paris St-Germain ta dauki dan kwallon tawagar Faransa, Ousmane Dembele daga Barcelona kan fam miliyan 43.5.

Dembele, mai shekara 26, ya koma Barcelona daga Borussia Dortmund kan fam miliyan 135 a 2017 da cin kwallo 40 a wasa 185 da daukar La Liga uku.

Wanda ya lashe kofin duniya a 2018 World Cup ya amince da kwantiragin kaka biyar da kungiyar da ke kofin Ligue 1 na bara.

Dembele, wanda ya dauki Copa del Rey biyu ya saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a Barcelona kaka biyu a bara.

Tun farkon watan nan kociyan Barcelona, Xavi ya san cewar Dembele zai bar kungiyar Camp Nou.

Dembele ya buga wasan karshe a gasar kofin duniya a Qatar a Disamba, wanda jinya ta hana shi buga wasannin da yawa a Barcelona.

Ya buga wa Faransa wasa 37 da cin kwallo hudu, kuma shi ne na tara da PSG ta dauka kan fara kakar bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here