‘Yan sanda sun ceto mutum 5 da aka sace a Katsina

0
247

Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta ceto wasu mutum biyar da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a Karamar Hukumar Malumfashi da ke jihar.

Har ila yau, rundunar ‘yansandan kuma na ci gaba da bibiyar ‘yan ta’addan da suka tsere bayan kai harin domin binciko maboyarsu.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Katsina, ASP Abubakar da ya tabbatar da faruwar lamari, ya bayyana cewa, jami’an ‘yansanda sun samu labarin cewa ‘yan ta’adda masu yawan gaske, sun kai hari kauyen Sabon Gida da ke Karamar Hukumar da sanyin safiya inda suka yi garkuwa da mutanen.

Ya kara da cewa daga baya ‘yan ta’addar sun yi ta matsawa wadanda suka yi garkuwa da su din kan su tafi zuwa Kankara a lokacin da jami’an tsaro suka tunkaro yayin da suke artabu da su.

Aliyu ya bayyana cewa, “A ranar 6 ga Agustan 2023, da misalin karfe 5 na safe, an samu labarin shigowar wasu ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai da suka hada da bindigar AK-47, inda suka yi ta harbe-harbe babu kakkautawa, sun kai hari kauyen Sabon Gida, a Karamar Hukumar Malumfashi, inda suka yi garkuwa da mutane biyar 5.

Hakan ya tursasa wa jama’a tserewa zuwa Karamar Hukumar Kankara domin tsira da ransu. Bayan samun rahoton ne kuma, ba tare da bata lokaci ba DPO na Kankara ya tara dakarunsa inda suka isa zuwa wurin, yayin da suka yi artabu da ‘yan ta’addar wanda dalilin hakan ya sa aka yi nasarar fatattakar su gami da kubutar da duk wadanda aka yi garkuwa da su.

“A halin ana nan ana ta kokarin kamo wadanda ake zargin bayan da suka tsre cikin daji.

“Bincike yana tafiya,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here