Barcelona za ta ɗauki Jao Cancelo

0
144

Chelsea ta shirya ƙara yawan kudin da za ta sayi ɗan wasan Brighton Moises Caicedo bayan Liverpool ta taya shi fan miliyan 111.

Kuɗin da ake tsammanin Chelsea za ta ƙara zai kai fan miliyan 115.Chelsea na dab da cimma yarjejeniya kan ɗan wasan Southampton mai shekara 19 Romeo.

Ita ma Liverpool har yanzu na nuna sha’awarta kan ɗan wasan Lavia kuma ana tsammanin za ta ci gaba da tattaunawa da Southampton kan shi.

Shirin Chelsea na sayam ɗan wasan Amurka Tyler Adams daga Leeds kan kuɗi fan miliyan 20 ya ɓaci.

Manchester City na shirin ƙara miƙa tayinta kan ɗan wasan tsakiya na West Ham Lucas Paqueta, bayan kin amincewa da tayin da ta yi na fan miliyan 70 ɗan ɗan wasan Brazil ɗin mai shekara 25 tun da fari.

Hammers na son City ta biya fan miliyan 90 kan ɗan wasan Brazil ɗin.

Idanun Barcelona ya koma kan ɗan wasan bayan Manchester City Jao Cancelo, a yanzu dai dillalin ɗan wasan na shirin shirya wannan ciniki.

Har yanzu Aston Villa na jiran amsa daga Galatasaray kan ɗan wasan Italiya Nicolo Zaniolo, da ta nema aro a kan fan miliyan 3 amma da zaɓin biyan fan miliyan 20 idan za a sayar mata da shi.

Arsenal ta yi shirin biyan fan miliyan 30 ga ɗan wasan bayan Japan Takehiro Tomiyasu mai shekara 30 wanda Inter Milan ta fara nuna shawa’arta a kan shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here