Masallacin Zaria ya rufta kan masallata, ya hallaka mutane 4

0
199

Akalla mutum hudu ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon ruftawar Babban Masallacin Zaria da ke Jihar Kaduna.

Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wadanda abun ya shafa suna tsaka da sallar La’asar ce yayin da ginin masallacin ya rufta kansu.

Sarki Bamalli ya ce tun a jiya Alhamis ce suka lura da yadda ginin masallacin ya tsage kuma suka shirya neman kwararrun injiniyoyin gine-gine domin yi wa tufkar hanci.

Sai dai ya ce tsautsayi wanda ba ya wuce ranarsa ya sanya wannan lamari ya faru tun gabanin a dauki matakin da ya dace.

Yayin da yake jajanta wa ’yan uwan wadanda lamarin ya shafa, Sarkin ya umarci a dawo gabatar da sallah a wajen masallacin har zuwa lokacin da za a kammala gyare-gyare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here